Kamaru-Ghana

Tilas a baiwa mazauna kudancin Kamaru kariya - Rawlings

Tsohon shugaban kasar Ghana John Jerry Rawlings.
Tsohon shugaban kasar Ghana John Jerry Rawlings. ISSOUF SANOGO/AFP/Getty Images

Tsohon Shugaban kasar Ghana JJ Rawlings ya bukaci Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar kasashen Afirka ta AU da su tashi tsaye wajen ceto mazauna kudancin Kamaru dake fuskantar ukuba daga hannun gwamnatin kasar.

Talla

A sakon da ya rubuta a shafin sa na yanar gizo, Rawlings yace abin takaici ne yadda Amurka da Birtaniya da kawayen su suka kauda kai a daidai lokacin da ake cin zarafin mutanen Yankin musamman ganin irin faifan bidiyon azabtarwar dake fitowa daga wurin.

Tsohon shugaban yace ganin yadda Faransa ke da dakaru a Mali, ya dace ace shugaba Emmanuel Macron ya dauki matakin kawo karshen matakin da gwamnatin Kamaru ke dauka.

Rawlings ya zargi kafofin yada labaran duniya da kungiyar kasashen Afirka da kauda kai dangane da abinda ke faruwa a Kamaru, inda ko Allah wadai basa iya fitowa su yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.