Najeriya ta gaza wajen kula da kananan yara - UNICEF

Logon Hukumar kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF
Logon Hukumar kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF

Hukumar Kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF ta bayyana Najeriya a matsayin daya daga cikin kasashe 6 da suka gaza a duniya wajen kula da rayuwar kananan yara ta fuskar kiwon lafiya da bada ilimi da samun abinci mai gina jiki.

Talla

Rahotan UNICEF yace daga cikin jerin kasashen duniya 180 da akayi nazari akan su,Najeria na matsayi na 174 a gaban kasashe irin su Afghanistan da Saliyo da Sudan ta kudu.

Rahotan da aka yiwa lakabi da ‘Makomar yara kanana a shekaru Masu zuwa’ ya gudanar da bincike a daukacin kasashen duniya 180 wajen tattara bayanai da kuma kwatanta su da cibagan da ake samu a kowacce kasa.

UNICEF tace sakamakon binciken da akayi ya nuna cewar makomar yara kanana da matasa a fadin duniya na fuskantar barazana daga bangaren sauyin yanayi da lalacewar muhalli da yadda yan jari hujja ke samar da abinci mara inganci irin su lemun zaki, abinci, giya da taba sigari da ke musu illa.

Rahotan yace babu wata kasa guda a duniya dake samar da tsaron da ya dace gay ara kanana wajen kula da lafiyar su da samar musu da muhalli mai inganci da kuma makoma mai kyau.

Alkaluman hukumar sun nuna cewar yaran dake kasashen Norway da Koriya ta kudu da Netherlands sun fi samun kariyar da zata basu damar rayuwa ba tare da matsala sabanin wadanda ke Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Chadi da Somalia da Jamhuriyar Nijar da kuma Mali saboda matsalolin da suke fuskanta.

UNICEF ta bayyana kasashe 10 dake sahun gaba a rahotan ta da suka kunshi Norway da Koriya ta kudu da Netherlands da Faransa da Ireland da Denmark da Japan da Belgium da Iceland da kuma Birtaniya.

Kasar Amurka na matsayi na 39 a cikin wannan rahoto, yayin da kasashe 10 dake matakin karshe suka hada da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Chadi da Somalia da Jamhuriyar Nijar da Mali da Guinea da Najeriya da Sudan ta kudu da Saliyo da kuma Afghanistan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI