Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

Kiir da Machar sun sha alwashin gaggauta magance yakin Sudan ta kudu

Shugaba Salva Kiir na Sudan ta kudu da Mataimakinsa Riek Machar.
Shugaba Salva Kiir na Sudan ta kudu da Mataimakinsa Riek Machar. Majak Kuany / AFP
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
Minti 2

Shugaba Salva Kiir da mataimakinsa Riek Machar na Sudan ta kudu sun sha alwashin daidaita al’amuran tsaron kasar ta hanyar kawo karshen yakin basasar da ya saro asali daga rikicin kabilanci.

Talla

A bikin murnar hadin kan bangarorin biyu da kuma sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiyar kasar da ya gudana a Juba babban birnin kasar, Mataimakin shugaban kasar ta Sudan ta kudu Riek Machar da ke matsayin tsohon madugun ‘yan tawaye ya sha alwashin mara baya ga tsare-tsaren gwamnati don alfanun al’umma.

Cikin shekaru 6 da Sudan ta kudu ta na fuskantar rikicin mai alaka da kabilanci akalla mutane dubu dari 4 sun rasa rayukansu yayinda mutane miliyan guda saka rasa matsugunansu.

Shima a jawabinsa yayin taron Salva Kiir ya ce ya zama wajibi bangarorin da ke rikici da juna a kasar u yafewa juna tare da rungumar juna don ciyar da kasar gaba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.