Togo

Gnassingbe ya lashe zaben Togo

Shugaba Faure Gnassingbé a lokacin da ya kada kuri'arsa
Shugaba Faure Gnassingbé a lokacin da ya kada kuri'arsa RFI/Peter Dogbe

Hukumar Zabe ta Togo ta bayyana shugaba Faure Gnassingbe a matsayin wanda ya lashe zaben da aka yi a karshen mako, duk da korafin tafka magudi da abokin karawarsa ya yi.

Talla

Hukumar zaben ta ce shugaba Gnassingbe ya samu kashi 72 na kuri’un da aka kada, yayin da abokin karawarsa kuma tsohon Firaminista Agbeyomi Kodjo ya samu kashi 18.

Dama tun kafin zaben an yi hasashen cewar Gnassingbe zai samu nasarar yin wa’adi na 4 da kuma ci gaba da mulkin iyalan gidansu duk da zargin da talakawa ke yi kan kuncin rayuwa.

Shugaba Gnassingbe ya karbi ragamar tafiyar da Togo tun daga shekarar 2005 sakamakon mutuwar mahaifinsa Gnassingbe Eyadema wanda ya jagorancin kasar na shekaru 38.

A watan Mayun bana, shugaban ya sauya kundin tsarin mulki wanda ya ba shi damar sake tsayawa takara, abin da ya haifar da zanga-zanga a cikin kasar.

Kafin bada sakamakon zaben a hukumance, Kodjo wanda ya yi wa mahaifinsa Firaminista ya ce, shi ya samu nasara da kashi 57 zuwa 61 na kuri’un.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.