'Yan kasar Kamaru sunyi tir ta kalaman Macron

Shugaban kasar Kamaru Paul Biya tare da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron yayin wata ganawa a Paris
Shugaban kasar Kamaru Paul Biya tare da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron yayin wata ganawa a Paris RFI Hausa

Daruruwan matasa a Kasar Kamaru sun gudanar da zanga zangar lumana zuwa ofishin Jakadancin Faransa domin nuna bacin ran su da kalaman shugaban Faransa Emmanuel Macron wanda ya yi alkawarin matsin lamba kan shugaba Paul Biya dangane da tsare wasu mutane da kuma kawo karshen rikicin yankin ‘yan aware da ake amfani da turancin ingilishi.

Talla

Rahotanni sun ce akalla matasa tsakanin 400 zuwa 600 ne suka shiga zanga zangar lumanar dauke da allunan dake da rubuce rubuce, inda suka dinga rera wakokin goyan baya ga shugaba Paul Biya, yayin da suke samun kariyar jami’an tsaro.

Kamfanin dillancin labaran Faransa yace matasan dake dauke da tutar Kamaru na shaidawa shugaba Macron cewar Kasar ba yankin Faransa bane, saboda haka ya daina katsalandan a ciki, tare da neman afuwar al'ummar Kamaru.

A ranar Asabar 22 ga watan Fabarairu ne wani faifen bidiyo ya bayyana a shafukan sada zumuntar intanet, wanda ya nuna shugaban Faransa Emmanuel Macron na sauraron wani da ya kira kansa dan gwagwarmayar Kamaru mazaunin Paris, inda ya zargi shugaba Paul Biya da aikata kissan kare dangi a yankunan Arewa masu Yamma da Kudu Maso Yammacin kasar dake fama da rikici.

Hoton bidiyon ya nuna Macron na cewa yana iya bakin kokarinsa wajen matsawa shugaba Biya lamba don magance matsalar kamar yadda ya yi lokacin da aka tsare jagoran adawar kasar Maurice Kamto.

"Ina iya bakin kokari na wajen ganin an samu kwanciyar hankali a kasar Kamaru, a lokacin da Paul Biya ya tsare Maurice Kamto na ce masa baza mu gana da shi a taron Lyon ba sai har ya sallami Kamto kuma hakan ya yi, don haka zan ci gaba da yi masa matsin lamba har sai ya kawo karshen rikicin", inji mista Macron.

Da take maida martani dangane da batun, gwamnatin kasar Kamaru cikin wata sanarwa dauke da sa hannun ministan sadarwar kasar Rene Emmanuel Sadi, ta yi Allah wadai da kalaman na mutumin da ke kiran kansa dan gwagwarmayar Kamaru, ba tare da nuna damuwa kan kalaman na Emmanuel Macron ko maida masa martani kai tsaye ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI