Nijar-Boko Haram

Nijar ta mikawa Najeriya tubabbun mayakan Boko Haram

Wasu daga cikin yan Boko Hraram da suka tuba
Wasu daga cikin yan Boko Hraram da suka tuba Daily Post

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta mikawa Najeriya tubabbun mayakan kungiyar boko haram 25 da suka aje makaman su.Tuni akayi jigilar wadannan mutane 25 zuwa Maiduguri a karkashin jagorancin Janar Bamidele Ashafa, babban jami’in dake kula da shirin horar da irin wadannan mutane.

Talla

Janar Ashafa yace zasu mika wadannan mutane 25 ga gwamnatin Jihar Barno domin kula da su.

Janar Ashafa yace zasu cigaba da karfafawa irin wadannan mutane gwuiwa domin ganin sun aje makaman su, domin rungumar shirin gwamnatin Najeriya na zaman lafiya.

Kwamishiniyar kula da harakokin mata a Jihar Barno da ta karbe su tace zasu ciyar da su da tufatar da su da kuma sake tunanin su tare da koya musu sana’oi a cibiyar da gwamnan jihar Farfesa Babagana Zulum ya samar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.