Mali-Faransa

"Rashin da'a da aiki tukuru ya janyowa sojin Faransa kyama a Mali"

Wasu sojojin Faransa dake aikin samar da tsaro a kasar Mali.
Wasu sojojin Faransa dake aikin samar da tsaro a kasar Mali. Ouest-France

Jakadan Mali a Faransa, ya yi kakkausar suka ga wani rukuni na sojojin da ke aiki karkashin rundunar tsaro ta Barkhane da ke aiki a kasar ta Mali, inda ya ce halayen wasu daga cikin sojojin ne babban dalilin da ya sa ake nuna wa Faransawa kyama a kasar.

Talla

Jakada Toumani Djirme na karba tambayoyi ne daga ‘yan majalisar dattawan Faransa wadanda suka gayyace shi domin bayyana rashin jin dadinsu dangane da yadda ake nuna wa Faransa kyama a Mali.

Jakadan ya ce zargin nuna kyama ga Faransa ba gaskiya ba ne, to sai dai ya ce al’ummar Mali nuna takaicinsu ne a game da kasantuwar dubban sojojin amma ba tare da sun magance kashe-kashen da ake yi wa jama’ar kasar ba.

Jakadan ya ce idan ka zagaya a cikin birnin Bamako, za ka ga sojojin rundunar ta Barkhane na yawo a cikin al’umma cikin yanayi na tsiraici wasu da zanen da ake kira Tatu a jikinsu, abin da ke kara zubar da kima da mutuncin da aka san sojojn Faransa da shi a baya.

Shi dai shugaba Ibrahim Boubacar Keita ya zargi masu kira da a kori sojojin ketare daga kasar ta Mali a matsayin wadanda ke mara wa ta’addanci baya, to sai dai jakada Djirme ya ce wasu daga cikin dabi’un sojojin ne suka janyo wa dakarun na Barkhane baki jini tsakanin al’umma.

Da aka nemi jakadan karin bayani game da shirin shiga tattaunawa tsakanin gwamnatin Mali da ‘yan ta’adda, jakadan ya ce tabbas za a tattaunawa, to sai ya ce jan layi, domin kuwa gwamnati ba za ta mika kan kowadanne bukatu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.