Wasanni

FC Barcelona zata kara da Real Madrid a El Classico

FC Barcelona zata kara da Real Madrid a El Classico
FC Barcelona zata kara da Real Madrid a El Classico Reuters/Andrew Couldridge

Yau da maraice kungiyar Real Madrid zata karbi bakuncin FC Barcelona a karawar da ake yiwa lakabi da El Classico da zai gudana a Madrid.Wannan karawar a kowacce shekara kan janyo hankalin kasashen duniya saboda muhimmancin ta ga kungiyoyin biyu da kuma magoya bayan su a kasashen duniya.

Talla

Bincike ya nuna cewar akalla mutane miliyan 80 kan kalli irin wannan karawar kai tsaye lokacin da ake yin ta a kasashen Duniya.

Yanzu dai haka FC Barcelona ke matsayi na farko a tebur da maki 55, yayin da Real Madrid ke matsayi na 2 da maki 53.

Samun nasarar Madrid zai bata damar komawa matsayi na farko, yayin da samun nasarar Barcelona zai sa ta baiwa Madrid tazara da maki 5.

Tarihi ya nuna cewar Barcelona ce tafi kowacce kungiya samu nasara kan Real Madrid, adadin da ya kai 72, yayin da ita ma Real Madrid ta zama kungiya daya tilo da ta doke Barcelona har sau 72.

Ko yaya kuke kallon karawar yau zata kaya?

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.