Najeriya za ta hukunta duk wanda ya kawo cikas kan rufe iyakokinta
A wani mataki na tabbatar da cewa iyakokin Najeriya sun ci gaba da kasancewa a garkame, shugaban kasar Muhammadu Buhari ya umurci da a gaggauta janye jami’an tsaron da ke yin zagon kasa ga manufar rufe iyakokin.
Wallafawa ranar:
A wata sanarwa da kakakin gwamnatin, Femi Adesina ya raba a birnin Abuja, shugaba Buhari ya umurci hukumomin tsaron da ke da ruwa da tsaki a sha’anin kula da iyakokin da su yi hukuncin da ya dace ga duk wani jami’insu da aka samu da laifin yin kafar ungulu a aikin tsaron iyakokin.
A shekarar da ta gabata ne gwamnatin kasar ta rufe iyakokinta, lamarin da ya janyo cece kuce a ciki da wajen kasar, duba da irin kalubalen da matakin ya taho da su.
Kwamitin da shugaban kasar ya nada don binciko batun zagon kasa ga kudirin rufe iyakokin kasar, a karkashin mai baiwa shugaban shawara a fannin tsaro Janar Babagana Munguno ya shawarci da a hukunta duk jami’in soji ko na farar hula da aka samu da hannu wajen kawo cikas a tsaron kan iyakokin, da rufe iyakokin ma.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu