Coronavirus

Coronavirus ta sake yaduwa a kasashen Afrika

Wani Bafaranshe ne ya shigar da Coronavirus cikin Senegal
Wani Bafaranshe ne ya shigar da Coronavirus cikin Senegal REUTERS/Ari Jalal

Hukumomin Senegal sun sanar da samun wanda ke dauke da cutar Coronavirus na farko a cikin kasar, abin da ya sanya kasar ta zama ta biyu a Afrika ta yamma da aka samu cutar da ke ci gaba da yaduwa kamar wutar daji.

Talla

Ministan lafiya Diouf Sarr ya shaida wa manema labarai cewar, wani Bafaranshe  da ya ziyarci kasarsa a watan jiya ne aka gano yana dauke da cutar, kuma yanzu haka an killace shi a Cibiyar Pasteur da ke birnin Dakar.

Sarr ya ce, mutumin wanda ya kwashe sama da shekaru 2 yana zama a Senegal ya koma Dakar ne a ranar 26 ga watan jiya bayan ya ziyarci Nimes da ke kudancin Faransa.

Ita ma kasar Tunisia ta sanar da samun mai dauke da cutar, abin da ya kawo adadin kasashen Afrika da suka kamu da cutar zuwa 5.

Kasar Saudi Arabia da a makon jiya ta sanar da dakatar da zuwa Umrah saboda barazanar yada cutar, ta ce an samu mutum guda dake dauke da ita yanzu haka.

Hukumomin kasar sun ce, mutumin wanda ya shiga kasar daga Bahrain yana samun kula a wani asibitin da aka killace shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI