Burkina Faso

'Yan bindiga sun kashe jami'an tsaro 10 a Burkina Faso

Tankokin yakin dakarun wanzar da zaman lafiya na rundunar Barkhane a kauyen Gorom-Gorom kasar Burkina Faso.
Tankokin yakin dakarun wanzar da zaman lafiya na rundunar Barkhane a kauyen Gorom-Gorom kasar Burkina Faso. AFP/Michèle Cattani

‘Yan bindiga sun kashe ‘yan sandan Burkina Faso akalla 10 a garin Sebba, cibiyar gwamnatin lardin Yagha dake arewacin kasar mai makotaka da Mali.

Talla

Sanarwar da mahukunta suka fitar tace baya ga wadanda suka rasa rayukansu, akwai wasu ‘yan sanda da dama suka jikkata harin da aka kai ranar asabar da ta gabata.

Rahotanni sun ce adadi mai yawa na mahara ne suka kai mummunan farmakin da nufin murkushe sansanin sojin na Burkina Faso da wani ofishin ‘yan sandan kasar dake birnin na Sebba.

A makon farko na watan Fabarairu ‘yan bindiga sun kaiwa garin na Sebba mai iyaka da Nijar farmaki, inda suka kashi mutum guda, tare da sace mutane 7.

Cikin shekarar 2015 Burkina Faso wadda tayi iyaka da Mali da kuma Nijar, ta soma fuskantar hare-haren ta’addancin da suka salwantar da rayukan sama da mutane 800, da kuma raba wasu dubu 800 da muhallansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI