Kotun koli a Najeriya ta yi watsi da karar Jam’iyyar PDP a Jihar Imo
Kotun Kolin Najeriya tayi watsi da karar da Jam’iyyar PDP da dan takarar ta na Gwamnan Jihar Imo Emeka Ihedioha suka shigar inda suke bukatar sauya hukuncin da ya baiwa Jam’iyyar APC kujerar Gwamnan Jihar.
Wallafawa ranar:
Alkalan kotun kolin guda 7 a karkashin jagorancin shugabanta Tanko Muhammad suka amince su yi watsi da karar ba tare da hammaya ba.
Mai shari’a Olukayode Ariwoola ya karanta hukuncin na yau, inda yace bukatar da Jam’iyyar PDP da dan takarar ta suka shigar bashi da tasiri, saboda haka tayi watsi da ita.
Sai dai alkakin ya ki cin tarar masu gabatar da karar kamar yadda aka gani a hukuncin Jihar Bayelsa da kotun ta gabatar.
Idan dai ba’a manta ba, kotun koli ta karbe kujerar gwamnan jihar Imo daga hannun Emeka Ihedioha na Jam’iyyar PDP inda ta mikawa Hope Uzodinma na APC ranar 14 ga watan Janairu, bayan Ihedioha ya kwashe sama da wata shida yana mulkin jihar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu