Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

Ra'yoyin masu sauraro kan yadda al'amuran tsaro ya tabarbare a Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. REUTERS/Siphiwe Sibeko

Al’amuran tsaro na cigaba da tabarbarewa a Najeriya, inda ko a karshen makon da ya gabata akalla mutane 50 yan bindiga suka hallaka a wasu kauyuka 4 dake karamar hukumar Igabi da Giwa na jihar Kaduna.Wannan na zuwa ne a yayin da gwamnati ke ikirarin daukar matakan kare rayuka da kuma dukiyoyin al’umma a sassan Kasar.Me za ku ce game da wannan hali da Najeriya ta sami kanta?Ko kun gamsu da matakan da gwamnati ke dauka a bangaren tsaro a Najeriya?Masu sauraro sun ba da ra'ayoyinsu a cikin shirin Umma Yunusa ta gabatar.

Talla

Ra'yoyin masu sauraro kan yadda al'amuran tsaro ya tabarbare a Najeriya

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.