Najeriya-Tsaro

‘Yan bindiga: ba ku isa ku hana 'yan Najeriya sakat ba – Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya caccaki kisan mutane sama da 50 da ‘yan bindiga suka yi a Kaduna, inda ya gargadesu da kada su yi tunanin za su iya hana al’umma sakat da wajen aikata ta’addanci.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. oodweynemedia
Talla

Buhari ya shaida wa ‘yan ta’addan cewa akwai gwamnatin da al’umma ta zaba don kare ta, kuma ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen taka musu birki.

Shugaban na Najeriya ya ce gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin ta bi ‘yan bindigar har maboyarsu ta kamo su don hukunta su.

A wata sanarwa da kakakin shugaban kasar Garba Shehu ya bayar, shugaba Buhari ya sha alwashin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da farauto ‘yan bindiga ta wajen atisayen soji da ake yi a jihar ta Kaduna a halin yanzu.

Yayin da yake bayyana takaicinsa kan harin da aka kai, shugaban ya ce ‘yan bindigar sun harzuka ne da atisayen soji da ake yi a Kaduna, shi ya sa suke hucewa a kan al’umma, amma hakan ba zai sa gwamnati ta yi kasa a gwiwa ba, har da zai kai ga dakatar da atisayen sojin.

Buhari ya jajanta wa al’ummar da suka fuskanci wannan harin, kana ya tabbatar musu da cewa gwamnati za ta yi duk mai yiwuwa wajen kare su.

A ranar Lahadi ne wasu ‘yan bindiga suka kai farmaki a wasu kauyuka a karamar Hukumar Igabi a jihar Kaduna, inda suka kashe mutane 51 tare da jikkata da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI