Amurka-Najeriya

Amurka tayi tayin ladar Dala miliyan 7 a kan Abubakar Shekau

Kasar Amurka tayi tayin bada ladar Dala miliyan 7 ga duk wanda ya bada labarin inda za’a kama shugaban kungiyar boko haram Abubakar Shekau.Kwamitin bada lada domin magance ayyukan ta’addanci na ma’aikatar harkokin wajen Amurka yayi tayin bada wadannan makudan kudade a sanarwar da yayi yau.

Abubakar Shekau, Shugaban kungiyar BOKO HARAM
Abubakar Shekau, Shugaban kungiyar BOKO HARAM AFP PHOTO / BOKO HARAM
Talla

Abubakar Shekau ya zama shugaban kungiyar boko haram tun bayan kisan gillar da aka yiwa shugaban kungiyar Muhamadu Yusuf a shekarar 2009.

Kungiyar boko haram tayi sanadiyar kashe dubban mutane da kuma raba akalla miliyan biyu da rabi da gidajen su a hare haren da suka kawashe sama da shekaru 10 suna kaiwa.

Daga cikin mutane sama da miliyan 2 da suka tsere daga muhallin su a Najeriya, akalla 250,000 sun samu mafaka a kasashen Kamaru da Chadi da Jamhuriyar Nijar.

Kungiyar tayi kaurin suna wajen garkuwa da mutane da kuma sace dalibai 276 a makarantar Chibok a shekarar 2014 da kuma sace sama da 100 a makarantar Dapchi, inda ta sako akasarin su banda Leah Sharibu da tace ta rike ta saboda taki sauya addinin ta.

Kungiyar ta kuma kai hare hare makarantu ciki harda kona daliban makarantar sakandaren Buni Yadi dake jihar Yobe da tada bama bamai a wuraren ibada da kasuwanni da wuraren taron jama’a a Jihohin Borno da Yobe da Adamawa da kuma wasu garuruwa daban daban da suka hada da kano da Bauchi da Plateau da Abuja.

Sau 3 dakarun Najeriya na ikrarin hallaka Abubakar Shekau amma kuma daga bisani sai a sake ganin sa ya bayyana cikin sakonnin bidiyo da yake fitar wa.

Abubakar Shekau ne mutumi na 8 cikin jerin sunayen Yan ta’addan da Amurka ke nema ruwa ajallo, wadanda kuma ta sanya kudade akan su.

Sauran sun hada da Ayman al-Zawahiri na kungiyar Taliban da aka sanya Dala miliyan 25 akan sa da Sirajuddin Haqqani na kungiyar Haqqani dake Pakistan da aka sanya Dala miliyan 10 akan sa da Abu Muhammad Al-Julani mai Dala miliyan 10, sai Abdullah Abdullah mai Dala miliyan 10 wanda ake zargin yana da hannu wajen harin da kungiyar Al Qaeda ta kai ofishin Jakadancin Amurka a shekarar 1998.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI