najeriya - coronavirus

Gindauniyar Dangote ta bada naira miliyan 200 domin yaki da cutar coronavirus

Hamshakin attajirin nahiyar Afrika, Alhaji Aliko Dangote.
Hamshakin attajirin nahiyar Afrika, Alhaji Aliko Dangote. REUTERS/Denis Balibouse

Gidauniyar Hamshakin attajirin Najeriya Aliko Dangote tayi alkawarin bada gudumawar naira miliyan 200 domin yaki da cutur coronavirus dake cigaba da hallaka rayukan jama’a a Duniya.

Talla

Jami’ar kamfanin Maryam Shehu Buhari ta sanar da tallafin a wajen taron gidauniyar da akayi a Abuja.

Wannan gudumawa itace mafi girma da wani mutum ya bayar domin yaki da cutar wadda aka samu mutum guda da ya kamu da ita a Najeriya.

Gidauniyar Aliko Dangote wadda ta bada naira biliyan guda wajen yaki da cutar ebola a Afirka na daga cikin sahun gaba gaba dake taimakawa wajen kula da lafiyar jama’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.