An kona kayar beguwar kurmi wato Pangolin a Cote D'Ivoire
Mahukunta a Cote d’Ivoire sun kona ton daya da rabi na kayar beguwar kurmi wato Pangolin, wanda aka kwace daga masu farauta ba a kan ka’ida ba a kasar.
Wallafawa ranar:
Kayar beguwar kurmi abu ce da ake matukar bukata musamman a kasashen Asiya, da suka hada da China da kuma Vietnam wadanda ke sarrafa magungunan gargajiya da shi, inda ake sayar da kilogram daya kusan dalar Amurka dubu daya.
Hukumomin na Cote D’Ivoire sun sanar da daukar matakan hukunta duk mutumen da aka sake kamawa da irin sassan jinkin wadanan namomin dawa a kasar.
Banda Cote D’Ivoire wasu kasashen Afrika irin su Najeriya na fama da irin wadanan matsaloli dake kawo koma baya ga tattalin arzikin su.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu