Majalisar dokokin Kano ta kaddamar da sabon bincike a kan Sarki Sanusi
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Majalisar dokokin Jihar Kano ta kaddamar da wani sabon bincike a kan Mai Martaba Sarki Sanusi na II saboda zargin sabawa dokoki da kuma al’adun Masarautar sakamakon wani korafi da aka gabatar mata.
Wani mai suna Mohammed Mukhtar na kungiyar bunkasa ilimi da kare al’adu ya gabatar da korafi ga Majalisar inda yake zargin yadda Sarkin ke tafiyar da al’amuran sa wadanda suka sabawa al’ada da addinin masarautar.
Wakilin mazabar Sumaila Zubairu Hamza-Masu ya karanta takardar korafin a zauren majalisar, yayin da shugaban Majalisar Abdulaziz Garba Gafasa ya bada umurnin mika korafin ga kwamitin kula da korafe korafen jama’a da ya gudanar da bincike akai.
Ana saran kwamitin wanda yake karkashin jagorancin mataimakin shugaban majalisar Hamisu Chidare ya kamala aikin sa a cikin mako guda domin gabatar da rahoto ga Majalisar da kuma shawara kan matakan da ya dace ta dauka.
Idan dai ba’a manta ba takaddama ta kaure tsakanin bangaren gwamnatin da Masarautar Kano dangane da rawar da Sarki Muhammadu Sanusi na II ke takawa, wadda ta kaiga kirkiro sabbin Masarautu guda 4 da kuma tuhumar Sarkin da kashe kudade ba bisa ka’ida ba.
Yunkurin Masarautar Kano na ganin kotu taki amincewa da sabbin Masarautun yaci tura, ganin yadda akayi watsi da karar da wasu masu rike da Sarautun Kano suka shigar a kotu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu