Sojin Najeriya sun kashe tarin mayakan Boko Haram a Damboa

Runduna ta 7 ta sojin Najeriya a  Damboa, jihar Borno.
Runduna ta 7 ta sojin Najeriya a Damboa, jihar Borno. STEFAN HEUNIS/AFP

Hukumomin Najeriya sun tabbatar da cewar dakarun sojin kasar sun yi nasarar murkushe wani hari da mayakan Bok0 Haram suka kai garin Damboa, inda suka kashe da dama daga cikin su da kuma kwace motoci 19 da maharan suka je da su.

Talla

Gwamnan Jihar Barno Farfesa Babagana Umara Zulum ya tabbatar da fafatawar da akayi a sanarwar da ya rabawa manema labarai wanda ke jinjinawa sojojin saboda rawar da suka taka.

Farfesa Zulum ya ce sojin sun taka rawar gani wajen fuskantar mayakan ta kasa da sama abinda ya basu nasarar kashe da dama daga cikin su da kuma kwace motoci 19.

Gwamnan ya ce ya zama wajibi ya yabawa dakarun Najeriya saboda rawar da suka taka wajen wannan arangamar da aka yi jiya laraba da safe lokacin da mayakan Boko Haram suka yi yunkurin mamaye garin Damboa baki daya.

Farfesa Zulum ya ce abinda ya fi faranta masa rai shine yadda sojojin suka bi mayakan wadanda suka tsere bayan anfi karfin su a Damboa, inda suka yi nasarar kashe wasu daga cikin su da kona motocin su guda 6.

Gwamnan ya kuma yaba wa 'yan sa kai da suka taka rawa wajen fuskantar maharan wanda ya kai ga mutuwar biyu daga cikin su.

Farfesa Zulum ya shaida wa al’ummar Jihar Barno cewar, ana daukar matakai da dama domin ganin an ga bayan wannan yaki na Boko Haram, kuma da taimakon Ubangiji za su samu nasara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.