Afrika ta Kudu

Afrika ta Kudu ta sanar da bullar annobar Coronavirus

Wasu daga cikin kayakin kariya daga kamuwa da cutar Coronavirus
Wasu daga cikin kayakin kariya daga kamuwa da cutar Coronavirus REUTERS/Eric Gaillard

A karon farko Afrika ta Kudu ta sanar da bullar annobar murar mashako ta Coronavirus baya ga wasu kasashen na Afrika da suka hada da Najeriya ,cutar dake ci gaba da bazuwa zuwa kasashen Duniya.

Talla

Ma’aikatar lafiyar kasar ta ce mutumin da ya kamu da cutar mai shekaru 38 bai jima da dawowa daga tattakin da yayi zuwa kasar Italiya tare da matarsa ba, wadanda ke cikin gungun matafiya 10 da suka dawo kasar ta Afrika ta Kudu ranar 1 ga watan Maris da muke ciki.

Wasu daga cikin kasashen Duniya sun sanar da haramta tarruruka a manyan wurrare a cikin kasashen .

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI