Ana zargin magajin garin Zinder da karkata kadarori mallakin al’umma

Birnin Damagaram ko Zinder  a jamhuriyar Nijar
Birnin Damagaram ko Zinder a jamhuriyar Nijar youtube.com

Wani takun saka ya barke tsakanin magajin garin Damagaram da wasu zababbu wakilan jama'a da kuma kungiyoyin kwadago, wadanda ke zargin magajin garin da waware kadarori mallakin al’umma, da suka hada da gidaje da filaye kai har ma da makabarta.

Talla

Jihar Damagaram ko Zinder na daya daga cikin jihohin kasar Nijar da ma'ikanta ke fuskantar tuhuma daga kungiyoyi masu zaman kan su.

Jama'a na fatan ganin Shugaban kasar Mahamadu Isufu ya aike da masu bincike don hukunta masu hannu a wannan kazamin aiki a jihar Damagaram dama wasu yankunan kasar ta Nijar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.