Ankai hari kusa da ofishin jakadancin Amurka dake Tunisiya

An kai harin kunar bakin wake a birnin Tunis na kasar Tunisia, inda maharan su biyu suka rasa rayukansu tare da raunata akalla mutane 6 ciki har da wadanda ke aiki tabbatar da tsaron ofishin jakadancin Amurka.

Yan sanda da jami'an kashe gobara a wurin da aka samu fashewa a Tunusia
Yan sanda da jami'an kashe gobara a wurin da aka samu fashewa a Tunusia Photo: Fethi Belaid/AFP
Talla

Fashewa ta faru ne a unguwar Berges du Lac da ke kunshe da mafi yawan ofisoshin jakadancin kasashen duniya ciki har da na Amurka, lamarin da ya haifar da tsoro da kuma guje-gujen jama’a.

Daya daga cikin maharan wanda ke kan babur ya yi yunkurin kutsawa a cikin ginin ofishin jakadancin na Amurka to sai dai jami’an tsaro suka kange shi.

Daga bisani dai wannan maharin ya mutu bayan da ya tarwatsa kansa ga alama da jigidar bama-bamai da ke jikinsa.

To sai dai sanarwar ta baya-bayan nan da ma’aikatar tsaron cikin gidan Tunisia ta fitar ta tabbatar da cewa maharan su biyu ne, kuma dukkaninsu sun mutu.

A wata sanawar da ya fitar, ofishin jakadancin Amurka ya tabbatar da faruwar lamarin tare da sanya jami’ansa a cikin shirin ko-ta-kwana.

Wannan dai shi ne karo na farko da birnin Tunis ya fuskanci harin ta’addanci tun bayan wanda aka kai a watan yunin shekarar bara, kuma tuni aka baza dimbin jami’an tsaro a birnin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI