Najeriya

Ba gaskiya bane cewa rundunar sojin Najeriya na daukar yan Boko haram

Wasu daga cikin tubabbun ‘yan kungiyar boko haram
Wasu daga cikin tubabbun ‘yan kungiyar boko haram Daily Post

Ma’aikatar tsaron Najeriya ta karyata rahotannin dake cewa rundunar sojin Kasar na daukar tubabbun ‘yan kungiyar boko haram aiki a matsayin sabbin dakarunta.Babban Hafsan rundunar tsaron Najeriya Janar Gabriel Olonisakin ne yayi sanarwar a wata ganawar masu ruwa da tsaki da ta gudana a babban birnin kasar Abuja.

Talla

Dubban yan kasar sun bayyana damuwa biyo bayan wannan labari,wanda ga baki daya ake hasashen zai iya rusa kokarin dakarun Najeriya a yakin da suke yi da yan Boko Haram.

A lokacin da muka nemi jin ta bakinsa daya daga cikin masana sha’anin tsaro a Najeriya Squadron Leader mai ritaya Aminu Bala Sokoto, ya ce abin da kamar wuya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.