Afrika

Coronavirus ta bulla a Kamaru

Jami'an kiwon lafiya a kasar Kamaru sun sanar da gano mutum daya dauke da cutar Coronavirus.Da safiyar yau juma'a ne ministan kiwon lafiyar Kamaru ya fitar da sanarwa dake tabbatar da gano wani bafaranshe mai dauke da cutar.

Masu bincike dangane da kwayar cutar Coronavirus
Masu bincike dangane da kwayar cutar Coronavirus AFP/Seyllou
Talla

Baya ga kasar Kamaru,hukumomin kiwon lafiya a Najeriya A Najeriya, kwamishinan lafiyar jihar Legas Farfesa Akin Aboyami ya tabbatar da killace wani karin mutum guda dan kasar da ya dawo daga Faransa kwanaki 3 da suka gabata, inda ake gudanar da bincike kan yiwuwar kamuwarsa da cutar Coronavirus, bayan nuna wasu alamu.

Yanzu haka dai mtumin na killace ne a asibitin lura da dakile yaduwar cutuka dake Yaba a jihar ta Legas, inda aka soma tsare mutum na farko a Najeriya da ya kamu da cutar Coronavirus wani dan kasar Italiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI