Najeriya

An gano ma’aikatan bogi dubu 70 a Najeriya

Gwamnatin Najeria tace ta gano ma’aikatan bogi dubu 70 cikin jerin sunayen ma’aikatan ta dake karbar albashi kowanne wata.Ministan kudin kasar Shamsuna Ahmed ta bayyana haka lokacin da take bude taron manyan jami’an Baitulmali da ma’aikatar kudi da masu binciken kudade a birnin Kano.

Zanga-zangar kungiyar ma'aikatan Najeriya
Zanga-zangar kungiyar ma'aikatan Najeriya
Talla

Shamsuna Ahmed tace gwamnati a shirye take ta kawar da duk wani ma’aikacin bogo dake cikin jerin ma’aikatan ta wajen yin amfani da tsarin biyan albashin da ake yiwa lakabi da IPPIS.

Duk da yake ministan bata bayyana irin matakan da suke dauka kan ma’aikatan da aka gano ba da kuma wadanda suka sanya sunayen su, tace gwamnatin su na iya bakin kokarin ta wajen samun nasarar kawar da matsalar baki daya.

Shamsuna Ahmed tace kawo sabon tsari irin wannan ya kan gamu da matsaloli daban daban, kamar yadda kungiyar malaman jami’oi suka bijirewa shirin na IPPIS.

Ministan tace ya zuwa yanzu kashi 55 na malaman jami’oi dake kungiyar ASUU sun yi rajistar shiga shirin, yayin da ta bayyana cewar duk wanda yaki ba zai samu albashi ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI