Sudan

Jami’an tsaron Sudan sun yiwa fararen hula akalla 241 kisan gilla

Mahukuntan Sudan sun amince da mika tsohon shugaban kasar Oumar al-Bashir ga kotun ICC. (14/02/2020)
Mahukuntan Sudan sun amince da mika tsohon shugaban kasar Oumar al-Bashir ga kotun ICC. (14/02/2020) RFI

Wani binciken jami’an kare hakkin bil Adam na kasa da kasa ya bankado cewar jami’an tsaron Sudan sun yiwa fararen hula akalla 241 kisan gilla, yayin murkushe masu zanga-zangar adawa da gwamnati cikin watan Yunin shekarar bara.

Talla

Murkushe masu zanga-zangar a wancan lokacin dai shi ne lamari mafi muni da aka gani a tsawon lokacin da dubun dubatar ‘yan Sudan suka yi suna zanga-zangar neman sauyin gwamnati da suka soma a karshen 2018, abinda ya kawo karshen mulkin tsohon shugaban kasar Omar El Beshir cikin watan Afrilun shekarar 2019.

Bayan kawar da El Beshir ne ranar 3 ga watan Yuni sojin Sudan suka afka da karfi fiye da kima kan masu zanga-zanga da suka yi zaman dirshe a harabar shelkwatar rundunar sojin kasar bisa neman su mikawa farara hula mulki

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI