Najeriya

Majalisar Dattijan Najeriya ta amince da karbo bashin dala biliyan 22

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. oodweynemedia

Majalisar Dattijan Najeriya ta amince da bukatar shugaban kasar Muhamadu Buhari na karbo bashin dala biliyan 22.Bayan cimma matsaya kan bukatar, shugaban Majalisar Dattijan Ahmad lawal ya ce za’a yi amfani da bashin wajen ayyukan raya kasa da kyautata rayuwar ‘yan Najeriya.

Talla

Bankunan da Najeriya ke sa ran karbo bashin na dala biliyan 22, sun hada da Bankin Duniya, Bankin Musulunci na Duniya, Bankin Raya kasashen Afrika, da kuma wasu bankunan na kasashen Japan, China da kuma Jamus.

Wasu daga cikin alkawuran da Shugaban Najeriya Muhamadu Buhari yayi a lokacin zabe sun hada da kyautata rayuwar yan Najeriya da kuma samar mnasu kayakin more rayuwa,wanda da dama daga cikin yan kasar suka bayyana cewa ya zuwa yanzu Gwamnatin kasar ta yi kasa a gwuiwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.