Najeriya

Yan Najeriya sun bayyana damuwa kan shirin ciwo bashi a kasashen Duniya

Yan Najeriya na cigaba da bayyana bacin ran su dangane da yadda Majalisar Dattawan kasar ta amince da shirin ciwo bashin kudin da ya zarce Dala miliyan 22 da rabi daga kasashen Duniya domin gudanar da ayyukan raya kasa.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a lokacin da yake sa hannu a takardar karbo bashi
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a lokacin da yake sa hannu a takardar karbo bashi Twitter: @BashirAhmaad
Talla

Cikin wadanda suka bayyana damuwar su da shirin ciwo bashin harda Jam’iyyar adawa ta PDP ta hannun Sakataren yada labaran ta Kola Ologbodian wanda yace amince da ciwo bashin ya dada nuna yadda Jam’iyyar APC mai mulki bata damu da halin da ‘yan Najeriya ke ciki ba.

Ologbodian wanda ya bayyana bashin a matsayin abinda zai dada mayar da ‘yan kasar bayi, yace abin takiaci ne yadda Majalisar ta amince da ciwo bashsn Dala miliyan 500 da sunan daga darajar tashar talabijin din NTA domin ganin yayi gogayya da tashoshin duniya irin su CNN.

Jam’iyyar tace a karkashin mulkin Buhari Najeriya ta dada tsunduma cikin basusukan da suka shake ta iya wuya ba tare da ganin abinda akayi da kudaden ba.

Wani masanin tattalin arziki Paul Alaje yayi bayani kan yadda Najeriya zata iya samar da kudaden da zata gudanar da manyan ayyuka ba tare da ciwo bashi daga kasashen ketare ba.

A nashi tsokaci, Musa Abdullahi na Jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria yace ya dace gwamnati ta mayar da hankali wajen ganin ta gano wadanda basa biyan haraji domin kara yawan kudaden shigar da take samu wadanda za tayi manyan ayyuka da su.

Shi kuwa Emmanuel Agabi, dan jarida nuna shakku yayi kan irin makudan kudaden da gwamnati ke kashewa ba tare da ganin ayyukan da akayi ba, inda ya bukaci gwamnatin da ta dinga sanya ido sosai kan jami’an ta dake kula da manyan ayyuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI