Najeriya

EFCC ta gurfanar da lauyan Atiku Abubakar a kotu

Shugaba Muhammadu Buhari da dan takarar babbar Jam’iyyar adawa Atiku Abubakar ne manyan ‘yan takarar shugabancin kasa. (2019-02-15)
Shugaba Muhammadu Buhari da dan takarar babbar Jam’iyyar adawa Atiku Abubakar ne manyan ‘yan takarar shugabancin kasa. (2019-02-15) Dr MEDDY

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ta EFCC ta sake gurfanar da Uyiekpan Giwa-Osagie, lauyan tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a kotu, inda take tuhumar sa da laifin halarta kudaden haramun da suka kai Dala miliyan 2 lokacin zaben shekarar 2019.

Talla

Jami’an hukumar EFCC sun kama Giwa-Osagie ranar 8 ga watan Agustan bara inda suka tuhume shi da laifuffuka 3 na halarta kudaden haramun a gaban alkali Nicholas Oweibo dake Lagos.

Hukumar tace tana tuhumar Giwa-Osagie da kanin sa Erhunse Giwa-Osagie da sarrafa Dala miliyan 2 ba tare da bin ka’idar hada hadar kudade ta kasa ba, wanda hakan ya sabawa doka.

EFCC tace hada hadar ta sabawa sashe na 18 na dokar halarta kudaden haramun na shekarar 2011.

Wadanda ake zargin sun ki amincewa da tuhumar da aka masu, yayin da lauyan su ya bukaci a bada belin su, amma alkali yace sai ranar litinin mai zuwa zai yanke hukunci a kai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.