Kamaru ta tsaida ranar karasa zaben ‘yan majalisa a yankunan ‘yan aware
Gwamnatin Kamaru ta bayyana 22 ga watan Maris da muke ciki a matsayin lokacin da za ta karasa gudanar da zabukan ‘yan majalisa a yankunan masu amfani da turanci Ingilishi, bayan tilasta dage su a watan Fabarairu, a dalilin rikicin ‘yan aware.
Wallafawa ranar:
Zabukan za su gudana ne a yankuna 11 dake lardunan masu amfani da Ingilishin a arewa maso yammaci da kuma kudu maso yammacin kasar ta Kamaru, domin cike guraben kujerun ‘yan majalisa 13.
Kafin zabukan su guda dai mayakan ‘yan awaren dake neman kafa kasar su, sun gargadi al’ummar yankunan da barazanar afkawa duk wanda ya kada kuri’a ko ya tsaya takara a zabukan na ‘yan majalisa da kananan hukumomi, lamarin da ya kai ga gwabza fada tsakaninsu da dakarun soji a lokuta daban daban.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu