Afrika

Ma’aikata sun yi zanga zanga a Burkina Faso kan haraji

Wasu daga cikin masu zanga-zanga a Burkina Faso
Wasu daga cikin masu zanga-zanga a Burkina Faso OLYMPIA DE MAISMONT / AFP

Dubban ma’aikata a Burkina Faso yau sun gudanar da zanga zanga domin nuna adawar su da shirin gwamnatin kasar na sanya haraji kan alawus din da ake biyan su. 

Talla

Wannan ya biyo bayan matakin da gwamnatin ta dauka na aiwatar da shirin harajin kan kudaden da ake biyan ma’aikatan daga watan jiya kamar yadda ake yiwa ma’aikatan dake yiwa kamfanoni aiki.

Rahotanni sun ce daga cikin ma’aikatan gwamnati 200,000 dake kasar, an ragewa akalla 190,000 albashin da ya kai Cefa 1,000 zuwa 5,000.

Yanzu haka kungiyoyin kwadago sun shirya tsunduma cikin yajin aiki kan lamarin daga ranar 16 ga wata zuwa 20 ga wata, yayin da za suyi gangami ranar 17 ga wata a birnin Ouagadougou.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.