Najeriya

Najeriya zata yi shekaru 20 ta na biyan bashi da ta karba

Naira ,takardar kudin Najeriya
Naira ,takardar kudin Najeriya Getty Images

A makon da ya gabata majalisar dattawar Najeriya ta amince shugaban kasar Muhammadu Buhari ya karbo rance na dalar Amurka miliyan 22.7, wadda hakan zai kai bashin da ake bin kasar kusan biliyan50 na dala, lamarin da ya sa wasu ‘yan majalisar da alu’ummar kasa ke ganin ba a duba batun da idon basira ba kafin a amince da shi.

Talla

Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari na neman bashin ne ruwa a jallo don ta rage radadin mastin tattalin arziki da kasar ta shiga tare da kuma cike gibin da ke akwai a kasafin kudin bana. Bugu da kari gwamnatin Najeriya na neman bashin ne don rage ratar da sauran kasashe suka ba ta wajen samar da ababen more rayuwa, musammamn ma ruwan sha da sufuri.

Kusan kashi 70 na wannan rance, wato sama da dala biliyan 17, zai fito ne daga bankin kasar China na EXIM Bank, bankin da ya shafe kusan shekaru 20 yana baiwa Najeriya rance.

Baya ga China, sauran wadanda zasu baiwa kasar rance dai sune: bankin duniya, wanda zai bada sama da dala bilyan biyu, ($2,854,000,000); sai bankin bunkasa kasashen Afrika wanda zai bada kusan dala biliyan biyu ( $1,888,950,000); akwai bankin Musulunci da za karbi sama da dala miliyan dari a gunsa ($110,000,000); da hukumar hadin kan kasashe ta Japan, wato Japan International Cooperation Agency (JlCA) da za ta bada dala miliyan 200 cif ($200,000,000); banki bunkasa kasashe na Jamus, wato, German Development Bank (KFW) shi ma zai bada dala miliyan dari 200 – ($200,000,000) sai hukumar bunkasa kasashe na Faransa; wato the French Development Agency (AFD) da zai baiwa Najeriya rancen sama da dala miliyan dari 400, ($480,000,000).

Baya ga wannan bashi da Najeriya za ta Ciyo, akwai wanda ta karba tun a shekarar 2002 daga China. Wannan rance da ake daf da ciyowa, da kuma wanda aka ciyo tuntuni, ya sa yanzu Najeriya za ta kwashe shekaru kusan ashirin tana biyan kudin ruwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI