Najeriya

An sake zaben Najeriya ta jagorancin kwamitin zaman lafiya na MDD

CAR,DRC,SOMALIA,NAJERIYA,Yaki na rutsawa da wadandan ba su san hawa ba
CAR,DRC,SOMALIA,NAJERIYA,Yaki na rutsawa da wadandan ba su san hawa ba Dr Meddy

Kasashen Duniya sun sake zaben Najeriya da ta cigaba da jagorancin kwamitin samar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya wanda ke da alhakin sa ido kan ayyukan samar da zaman lafiya da Majalisar ke kula da shi a kasashe daban daban.

Talla

Samson Itegboje, karamin Jakadan Najeriya a Majalisar ya bayyana wannan nasara a taron da wakilan kwamitin suka yi a birnin New York wanda shine karo na 48. Jami’in yace an zabi Canada ta zama mataimakiyar Najeriya sai kuma kasashen Argentina da Poland da Japan da Masar a matsayin yan Majalisu.

Tun daga 1972 Najeriya ke jagorancin wannan kwamiti mai matukar muhimmanci saboda amincewa da jagorancin ta inda koda yaushe aka zo zabe sai wakilan kwamitin su bata damar cigaba da jagorancin sa.

Shi wannan kwamiti ne ke da alhakin sake fasalin duk wani aikin samar da zaman lafiya da Majalisar Dinkin Duniya ke gudanarwa da kuma bada shawara wajen yiwa aikin gyaran fuska dangane da abinda ya shafi dakaru sama da 100,000 dake aiki a karkashin Majalisar da suka hada da sojoji da Yan Sanda da fararen hula a kasashe 125 na duniya.

Najeriya na daya daga cikin kasashe 15 na duniya da suka fi bada dakaru da yawa dake aikin samar da zaman lafiya a duniya, kuma itace ta 8 a Afirka.

Alkaluma sun nuna cewar najeriya ta bada gudumawar sojoji 2,170 a shekarar 2016 da suka hada da Yan Sanda 403 da sojoji 1,721 da masu horar da su 46.

Daga cikin kasashen da dakarun Najeriya ke aiki akwai Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo da Mali da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Lebanon.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.