Tashin hankali ya sa ‘yan kasar Mali tserewa daga kauyuka
Wani bincike a Mali yace tashin hankalin da ake cigaba da samu a kasar sakamakon hare haren Yan bindiga da masu ikrarin jihadi sun tilastawa daruruwan mutane tserewa daga kauyukan su domin samun mafaka a wasu garuruwa.
Wallafawa ranar:
Rahotanni sun ce yanzu haka mazauna kauyen Toou dake kusa da Sevare sama da 400 sun gudu sun bar garin su wanda ya zama kango, yayin da suka samu mafaka a makarantar Sevare.
Bayanai sun ce wadannan mutane sun mamaye azuzuwa guda biyu dake makarantar Sevare, inda maza suka mamaye aji guda, yayin da mata da yara kuma suka mamaye guda.
Mazauna kauyen Toou na daga cikin miliyoyin Yan kasar Mali da tashin hankali ya tilastawa barin kauyukan su a Yankin Sahel musamman kauyukan kasashen Mali da Burkina Faso.
Daya daga cikin wadannan mutane Housseini Karembe, mai shekaru 65 yace tun daga ranar 5 ga watan Janairu suka sa kafa suka gudu daga kauyen sun a Toou lokacin da kasar tayi fama da rikicin Yan kabilar Dogon mafarauta da kuma makiyaya wanda yayi sanadiyar rasa daruruwan rayuka.
Rikici a kasar Mali ya barke ne tun dag shekarar 2012 lokacin da Yan Tawayen Abzinawa suka mamaye yankin arewacin Mali wanda daga bisani ya kaiga kifar da gwamnatin Amadou Toumani Toure.
Tabarbarewar tsaro da kasha kasha ya sa gwamnatin Faransa tura dakarun ta sama da 5,000, yayin da aka kafa rundunar G5 Sahel da ya kunshi sojojin kasashen Mali da Nijar da Burkina Faso da Mauritania da kuma Chadi domin shawo kan matsalar amma har yanzu ana cigaba da samun hare hare.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu