Chadi

'Yan bindiga sun kashe mutane 5 a Chadi

‘Yan bindiga a Chadi sun kashe mutane 5 a wani farmaki da suka kai kan wani yanki na lardin Sila dake gabashin kasar mai iyaka da Sudan.

Wata mai kiwon shanu a garin Dosso.
Wata mai kiwon shanu a garin Dosso. AFP/Marco LONGARI
Talla

Rahotanni sun ce mutanen da ‘yan bindigar suka halaka, na kan hanyar dawowa ne daga cin kasuwa a yankin na Sila.

Cikin watan Janairun da ya gabata ne dai shugaban kasar Idris Deby y adage dokar ta bacin da ya kafa a yankin, bayan da yayi fama da rikicin kabilanci tsakanin manoma da makiyaya.

Yankin gabashin kasar ta Tchadi, wuri ne na kiwo da ke kan iyakar kasar Sudan kuma a 'yan shekarun baya-bayan ya kasance wani yanki da ake yawaita rikici tsakani makiyaya Larabawa da mazauna yankin 'yan kabilar Ouaddaiens kan batun filayen noma da wuraren kiwo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI