Nijar

Boko Haram ta dirar wa sojojin Nijar a yankin Diffa

Wasu sojojin jamhuriyar Nijar
Wasu sojojin jamhuriyar Nijar Warren Strobel/Reuters

Mayakan Boko Haram sun kai hari cibiyar sojin Jamhuriyar Nijar a karshen mako, irin san a farko tun bayan hare haren da aka samu a karshen shekarar da ta gabata.

Talla

Rahotanni sun ce maharan sun kai harin ne a sansanin sojin dake Chetima Wangou a yankin Diffa a cikin motoci dauke da muggan makamai.

Wani mazaunin yankin ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewar, wasu daga cikin sojojin sun samu raunuka kuma ana kula da su a asibitin Diffa.

Chetima Wangou karamin kauye ne dake da nisan kilomita 25 daga Diffa, kuma tun daga shekarar 2015 boko haram ke kai hare hare a yankin tafkin Chadi.

A watan Fabarairun bara, sojojin Nijar 7 aka kashe a wannan wurin lokacin da mayakan book haram suka kai hari.

Boko haram ta kashe mutane akalla 27,000 a cikin shekaru 10, yayin da ta raba mutane sama da miliyan biyu da muhallin su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.