Najeriya

Dan wasan Nasarawa United ya mutu a filin kwallo

Wani dan wasan kungiyar Nasarawa United dake Najeriya Chieme Martins ya yanke jiki ya fadi a karawar da suka yi yau da Katsina United inda ya mutu nan take.

Tambarin Hukumar kwallon kafar Najeriya
Tambarin Hukumar kwallon kafar Najeriya completesportsnigeria.com
Talla

Rahotanni sun ce dan wasan yayi karo ne da wani dan wasan Katsina lokacin da ake karawar, kuma duk kokarin da likitoci suka yi na ceto rayuwar sa yaci tura daga likitocin dake fili da kuma asibitin da aka ruga da shi.

Wannan mutuwa ta girgiza yan kallo da shugabannin kungiyar Nasarawa United da abokan karawar su ta Katsina United a gasar league na Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI