Burkina Faso

Dubban ma'aikata sun yi zanga-zangar adawa dokar haraji

Dubban ma’aikatan gwamnati a Burkina Faso, sun gudanar da zanga-zangar adawa da dokar karin harajin da aka kakaba musu.

Dubban ma'aikatan gwamnati a Burkina Faso yayin zanga-zangar adawa karin harajin da aka kakaba musu.
Dubban ma'aikatan gwamnati a Burkina Faso yayin zanga-zangar adawa karin harajin da aka kakaba musu. AFP Photo/OLYMPIA DE MAISMONT
Talla

Kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya ce akalla ma’aikatan dubu 10 zuwa 20 ne suka yi mamaye titunan birnin Ouagadougou yayin zanga-zangar ta jiya asabar, inda suka sha alwashin ganin bayan dokar da ta dora haraji kan kudaden alawus din da suke samu bayaga harajin da ake yankewa daga gundarin albashinsu.

Rahotanni sun ce kungiyoyin kwadago a Burkina Fason na shirin shiga yajin aikin gama gari daga 16 zuwa 20 ga watan Maris da muke ciki, domin adawa da sabon tsarin na biyan haraji.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI