Jamhuriyar Congo

Jamhuriyar Congo na bukatar dala miliyan 20 don yakar Ebola - WHO

Maihafiyar wani yaro da annobar Ebola ta halaka a birnin Beni na Jamhuriyar Congo.
Maihafiyar wani yaro da annobar Ebola ta halaka a birnin Beni na Jamhuriyar Congo. REUTERS/Goran Tomasevic/File Photo

A yayinda hankalin hukumomin lafiya da kasashe ya karkata kan yakar annobar murar Corona, ita kuwa Jamhuriyar Congo fafutukar kawo karshen annobar Ebola take yi har yanzu.

Talla

A baya bayan nan ne dai hukuma lafiya ta duniya, ta ce Jamhuriyar Congon na bukatar tallafin dala miliyan 20 don kawo karshen annobar ta Ebola da ta shafe watanni 19 tana kisa a kasar, inda ta halaka jimillar mutane dubu 2 da 264.

A talatar da ta gabata ne dai likitoci suka sallami mutum na karshe da ya warke daga cutar Ebolan a kasar, sai dai ba za a tabbatar da kawo karshen annobar a hukumance ba, sai bayan kwanaki 42 ba tare da samun wanda ta sake shafa ba.

Annobar ta Ebola da ta barke cikin watan Agustan shekarar 2018, ita ce makamanciyarta mafi muni da aka gani a Afrika karo na 2, bayan wadda ta halaka sama da mutane dubu 11 a yammacin nahiyar, tsakanin shekarun 2013 zuwa 2016.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.