Kamaru

An kai harin Bam a Bamenda na kasar Kamaru

Yankin  Bamenda na kasar Kamaru
Yankin Bamenda na kasar Kamaru Via social media, independently verified.

A Bamenda dake kasar Kamaru, akalla mutane 10 hade da jami’an tsaro ne suka samu munanan raunuka bayan fashewar bam a wurin da ake gudanar da bikin dangane da ranar mata a yau lahadi.

Talla

Lamarin ya wakana dai dai lokacin da gwaman yankin da tawagar sa suka iso wannan wuri, inda jama’a suka yi dandazo.

Hakan ya faru ne kwana daya bayan wani harin bam da aka kai a garin Galim inda aka samu asarar rayuka da suka hada da yan sanda biyu da jandarmomi biyu hade da wani farrar fula.

Yankin na Bamenda na daya daga cikin yankunan da yan aware ke amfani da su wajen kai hare-hare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.