An killace wani dan kasar Jamus da ya kamu da Coronavirus a Masar
Wani dan kasar Jamus dake yawon bude ido a Masar ya zama mutumi na farko da ya mutu a Afirka sakamakon kamuwa da cutar coronavirus wadda yanzu haka ta razana kasashen duniya.
Wallafawa ranar:
Hukumomin Masar sun bayyana mutumin a matsayin mai shekaru 60 wanda ya fara nuna alamun zazzabi lokacin da aka kwantar da shi a asibitin Hurghada ranar 6 ga watan nan.
Ma’aikatar lafiyar kasar tace mutane 45 ake zargin suna dauke da cutar, wadanda suka hada da yan kasa da bakin da suka kamu a wani jirgin ruwa.
Firaminista Mostafa Madbouli yace jirgin na dauke ne da mutane 171, wadanda suka hada da baki 101 da kuma 70 yan Masar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu