Najeriya

Najeriya ta soke layukan waya sama da miliyan 2 saboda dalilan tsaro

Hukumar sadarwar Najeriya ta sanar da soke layukan waya miliyan 2 da dubu 200 wadanda ake amfani da su ba tare da yi musu rajista kamar yadda dokar kasa ta tanada ba.

Kamfanonin sadarwa na Najeriya
Kamfanonin sadarwa na Najeriya
Talla

Shugaban hukumar Farfesa Umar Danbatta ya sanar da daukar matakin wanda yace ya shafi layukan kamfanonin sadarwa da dama.

Farfesa Danbatta yace hukumar san a kokari wajen ganin cewar kowanne layin waya daga cikin miliyan 184 da aka yiwa rajista na dauke da bayanan masu amfani da su da ake iya tantancewa koda yaushe ba tare da samun matsala ba.

Shugaban hukumar ya sha alwashin cewar zasu dinga gudanar da bincike lokaci zuwa lokaci domin tabbatar da cewar ba’a sake samun irin wannan matsala ba.

Idan dai ba’a manta ba a watan Satumbar bara ministan sadarwa Dr Isa Ali Pantami ya baiwa hukumar umurnin tantance irin wadannan layuka da kuma soke su a matsayin daya daga cikin hanyoyin shawo kan matsalolin tsaron da suka addbi kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI