Somalia-Amurka
Rundunar Sojin Amurka ta kashe wani kwamandan Al Shebaab
Wallafawa ranar:
Rundunar Sojin Amurka dake aiki a Afrika ta sanar da kashe wani babban kwamandan kungiyar Al Shebaab a harin sama da ta kai musu.
Talla
Kanar Christopher Karns, Daraktan rundunar, ya bayyana sunan wanda aka kashe a matsayin Bashir Mohammed Mahmoud, wanda ake zargi da jagorancin hare hare a kasar Kenya.
Kanar Karns yace an kashe Bashir ne a ranar 22 ga watan jiya, kuma kafin hallaka shi ya jagoranci kai hari kan sansanin sojin Amurka dake Kenya a watan Janairu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu