Coronavirus ta yi kisan farko a Afrika
Wallafawa ranar:
Wani dan kasar Jamus da ke yawon bude ido a Masar ya zama mutum na farko da ya mutu a Afrika sakamakon kamuwa da cutar Coronavirus wadda yanzu haka ta razana kasashen duniya.
Hukumomin Masar sun bayyana mutumin a matsayin mai shekaru 60 wanda ya fara nuna alamun zazzabi lokacin da aka kwantar da shi a asibitin Hurghada ranar 6 ga watan nan.
Ma’aikatar Lafiyar kasar ta ce, mutane 45 ake zargin suna dauke da cutar, wadanda suka hada da 'yan kasa da bakin da suka kamu a wani jirgin ruwa.
Firaminista Mostafa Madbouli ya ce, jirgin na dauke ne da mutane 171, wadanda suka hada da baki 101 da kuma 70 'yan Masar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu