Burkina Faso

'Yan banga sun kashe mutane 43 a Burkina Faso

Wasu jami'an tsaron kasar Burkina Faso.
Wasu jami'an tsaron kasar Burkina Faso. AFP/Issouf Sanogo

Gwamnatin Burkina Faso ta tabbatar da rahoton mutuwar akalla mutane 43 da aka halaka yayin hare-haren da aka kaiwa wasu yankuna a arewacin kasar a ranar lahadin nan da ta gabata.

Talla

Wasu majiyoyi da suka shaida kai aukuwar lamarin sun ce jami’an tsaron sa kai na Vigilante ne suka kai jerin farmakin kan kauyukan Fulani da suka hada da Dinguila da Barga dake lardin Yatenga.

Majiyoyin sun ce jami’an na Vigilante sun kaiwa Fulanin farmakin ne bisa tuhumarsu da taimakawa mayakan ‘yan ta’adda dake kai hare-hare a sassan arewacin kasar ta Burkina Faso.

Sai dai sanawar da gwamnatin kasar ta fitar bata bayyana sunan kungiya ko wadanda take zargi da kai jerin hare-haren na baya bayan nan ba. Zalika ba ta bayyana cewar ko yankunan dafarmakin ya shafa yankunan Fulani bane.

A shekarar 2015 Burkina Faso ta soma fuskantar hare-haren ta’addanci wadanda a baya bayan nan suka janyowa Fulani makiyay tsangwama da kuma kai musu farmaki, sakamakon zarginsu da taimakawa mayakan ‘yan ta’adda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.