Afrika-Lafiya

Annobar Corona ta bulla a Burkina Faso da Jamhuriyar Congo

Wasu jami'an lafiya sanye da rigunan samun kariya daga cutar coronavirus.
Wasu jami'an lafiya sanye da rigunan samun kariya daga cutar coronavirus. REUTERS/Josiane Kouagheu

Kasashen Burkina Faso da Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo sun shiga cikin jerin kasashen duniya musamman na nahiyar Afrika da annobar murar Coronavirus ta shafa, wadda ke ci gaba da yaduwa cikin sauri zuwa sassan duniya.

Talla

Cikin sanarwar da ta fitar, gwamnatin Burkina Faso ta ce mutane 2 suka kamu da cutar murar sakamakon binciken likitocin daya tabbatar da hakan, bayan dawowarsu daga Faransa a ranar 24 na watan fabarairun da ya gabata.

Ma’aikatar lafiyar Burkina faso ta ce gwamnatin kasar ta kashe akalla euro miliyan 13 wajen daukar tsauraran matakai kan sama da matafiya dubu 13 dake zirga-zirga a filin jiragen saman kasar dake babban birnin kasar Ougadougou, domin dakile yaduwar cutar.

Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo ma dai a talatar nan ta bayyana samun mutum na farko da ya kamu da cutar a babban birnin kasar Kinsasha.

Ministan lafiyar kasar Eteni Longondo yace tuni aka killace marar lafiyan da ya kasance dan kasar Belgium a wani asibiti, yayinda aka matsa kaimi wajen gudanar da bincike don gano wadanda suka yi mu’amala da shi.

Kasashen afrika da a halin yanzu ke fama da annobar murar coronavirus sun hada da Masar, Morocco, Algeria, Kamaru, Najeriya, Senegal, Afrika ta Kudu, Togo, Burkina Faso da kuma Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.