Kano-Najeriya

Na yarda da hukuncin Allah a kaina - Sarki Sunusi

Tsohon Sarkin Kano mai martaba Alhaji Muhammadu Sunusi na biyu.
Tsohon Sarkin Kano mai martaba Alhaji Muhammadu Sunusi na biyu. YouTube/African Leadership Academy

Sarkin Kano da aka tsige, Muhammadu Sanusi II, ya ce ya karbi abin da ya same shi a matsayin wani hukunci na Allah.

Talla

A wani gajeren sakon bidiyo, Sanusi ya ce sauke shi daga kan karagar mulkin Kano shi ne mafi alkhairi a gareshi kamar yadda Allah ya tsara.

Sanusi, wanda ya taba rike mukamin gwamnan baban bankin Najeriya ya ce babu dalilin bacin zuciya don wannan al’amari da ‘Allah ya kaddari ya auku gareshi’.

A maimakon haka, tsohon sarkin ya bukaci al’umma da su kasance masu gode wa Allah a kullayaumin kan hukuincinsa a kan su.

Sanusi wanda ya ce Allah ne mai bada mulki a lokacin da ya so, ya kuma karbe a a lokacin da yake so, ya mika godiya ga Allah da damar shafe kusan shekaru 6 kan karagar mulkin Kano.

Ya bukaci wadanda ba su ji dadin abin da ya faru ba da su goya wa sabon sarki Aminu Ado Bayero baya, su kuma rungumi zaman lafiya.

Sanusi ya bayyana alfaharinsa ga salon shugabancinsa a zamaninsa a matsayin sarkin Kano, da kuma yadda kaddara ta sa abin da ya sami mahaifinsa ya same shi.

Ya gode wa al’umar jihar Kano da masu rike da sarautun gargajiya, jami’an fada, da abokansa sakamakon goyon baya da suka ba shi lokacin mulkinsa.

A ranar Litinin ne gwamnatin jihar Kano a Najeriya karkashin jagorancin Abdullahi Umar Ganduje ta tsige sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi II, bayan kusan shekaru 6 a kan kujerar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI