Afrika

Ecowas ta bukaci Guinea ta cire sunan wasu daga cikin rijistan zabe

Hotunan jam'iyyun siyasa a kasar Guinee Conakry
Hotunan jam'iyyun siyasa a kasar Guinee Conakry REUTERS/Stringer

Kungiyar kasashen Afirka ta Yamma ta bukaci hukumomin kasar Guinea da su cire sunayen mutane miliyan da rabi daga cikin rajistar masu zabe saboda kasa tantance su da akayi kafin zaben da za’ayi a kasar.

Talla

Wata tawagar kungiyar kwararru daga kungiyar ECOWAS da suka ziyarci Conakry domin taimakawa kasar shawo kan matsalolin zaben da take fuskanta ta dangane da zaben bayan korafi daga kasashen duniya ciki harda kungiyar Francophonie ta kasashe masu amfani da harshen Faransanci.

Hukumar zaben kasar tayi rajistar mutane sama da miliyan 7 da rabi ne, amma kuma sama da miliyan 2 da rabi sun kasa zuwa a tantance su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI