Najeriya

Jami'an tsaro sun kama 'yan bindiga sama da 100

Zaratan ‘yan sanda a Najeriya, karkashin runduna ta musamman da ke yaki da ayyukan ‘yan tsagera, wanda mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, Abba Kyari ke jagoranta sun kama wasu da ake zargi da aikata manyan laifuka su 105, da suka hada da masu garkuwa da mutane don karbar kudin fansa.

Jami'an tsaro Najeriya sun gabatarwa manema labarai miyagun mutane da suka kama
Jami'an tsaro Najeriya sun gabatarwa manema labarai miyagun mutane da suka kama RFI Hausa
Talla

Daga cikin masu laifin da aka gabatar wa ‘yan jarida a Larabar nan baya ga masu satar mutanen, har da masu samar musu da muggan kwayoyi da sauran abubuwan da suke bukata.

Sama da manyan bindigogi kirar AK 47 guda 50 ne aka karba a hannun wadanda ake zargin, da kuma motoci da babura da aka jirkita kirarsu, don boyewa, tare da jigilar manyan bindigogi.

Wadanda ake zargin sun amsa aikata laifin satar mutane da dama, tare da kisa a wasu jihohin Najeriya, inda suka ce su suka kai wa ayarin sarkin Potiskum hari, da wata motar luxurious, da wasu motoci, a kan hanyar Kaduna zuwa Zaria, inda suka sace mutane dayawa.

ACP Abba Kyari ya ce, runduna ta musamman na yin duk mai yiwuwa wajen gano mabuyar sauran masu aikata manyan laifuka a duk inda suke a Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI