Coronavirus

Coronavirus ta kama mutun na farko a Ivory Coast

Kasar Ivory Coast ta sanar da samun mutum na farko da ya kamu da sabuwar cutar Coronavirus, cutar da yanzu haka ta karade sassan duniya, ta kuma sanya fargaba a zukatan al’umma.

Kasashen Afrika na daukar matakan hana yaduwar Coronavirus
Kasashen Afrika na daukar matakan hana yaduwar Coronavirus REUTERS/Francis Kokoroko
Talla

Hukumomin kasar sun ce, wanda ya harbu da cutar wani dan kasar ne da bai dade da dawowa daga kasar Italiya ba.

Nahiyar Afrika dai ba ta dandana radadin wannan cuta da yanzu haka ta yadu har zuwa kasashe 110 tun da ta bulla a China a watan Disamban shekarar da ta gabata kamar sauran nahiyoyi duniya ba.

Dan kasar Ivory Coast din ya a harbu da cutar, wani mutum ne mai shekaru 45, wanda a ranar Talata aka ga alamomin cutar a tattare da shi, kuma da aka yi masa gwaji, aka same shi da cutar ta COVID-19 a cewar wata sanarwa daga ma’aikatar lafiya ta kasar.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, daga nan ne aka garzaya da mutumin asibiti, inda yanzu yake nuna alamun murmurewa.

Yanzu dai an gano dukkanin wadanda mutumin ya yi cudanya da su, kuma hukumomi na ta kokarin yin abin da ya dace ta wajen killace su.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce, ya zuwa yanzu mutane 20 ne suka harbu da wannan cuta a kasashen Kudu da saharar Afrika da suka hada da Afrika ta Kudu da Najeriya da Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo da Burkina Faso da Kamaru da  Senegal da kuma Togo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI